Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Zarif yana cewa, hadin kan da kasashen biyu suke yi dangane da fasahar biotechnology ko rayayyun halittu da kuma na kwayoyin halittu masu rai ko genetic yana da matukar muhimmanci.
A na shi bangare shugaban cibiyar binciken fasahar halittu masu rai na kasar Cuka ya bayyanawa nawa ministan inda aka tsaye a batun samar da alluran riga kafin cutar Covid-19 na hadin guiwa tsakanin kasar biyu.
Sannan ya jinjinawa ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran kan irin hadin kan da ta bawa kasar Cuba don ganin an gaggauta samar da alluran riga kafin cutar ta Covid- 19.
342/